logo HARUN YAHYA

Al-Ma`arij - ALQUR'ANI - Harun Yahya

  • 1. Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa.
  • 2. Ga kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa.
  • 3. Daga Allah Mai matãkala.
  • 4. Malã`iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne.
  • 5. Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo.
  • 6. Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa.
  • 7. Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa.
  • 8. Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa.
  • 9. Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi.
  • 10. Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake.
  • 11. Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa,
  • 12. Da matarsa da ɗan`uwansa.
  • 13. Da danginsa, mãsu tattarã shi.
  • 14. Da wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa`an nan fansar, ta tsĩrar da shi.
  • 15. A`aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã,
  • 16. Mai twãle fãtar goshi.
  • 17. Tanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai.
  • 18. Ya tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka.
  • 19. Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi.
  • 20. Idan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri.
  • 21. Kuma idan alhẽri ya shãfe shi, ya yi rõwa.
  • 22. Sai mãsu yin salla,
  • 23. Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne.
  • 24. Kuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne.
  • 25. Ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon.
  • 26. Da waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako.
  • 27. Da waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro.
  • 28. Lalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincẽwaba ce.
  • 29. Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne.
  • 30. Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne.
  • 31. To, duk wanda ya nẽmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka.
  • 32. Kuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne.
  • 33. Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgẽwa ne.
  • 34. Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarẽwa ne.
  • 35. Waɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne
  • 36. Mẽ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar (gudu).
  • 37. Daga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama`a-jama`a!
  • 38. Shin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni`ima ne (ba da wani aiki ba)?
  • 39. A`aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani.
  • 40. Sabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne.
  • 41. Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba.
  • 42. Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita).
  • 43. Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa.
  • 44. Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa.)
SHARE
Facebook
X
WhatsApp
Telegram
QR Code
QR Code